Buhari: Najeriya Zata Goyi Bayan Rage Yawan Man Da OPEC Take Haka
(last modified Thu, 21 Feb 2019 06:46:12 GMT )
Feb 21, 2019 06:46 UTC
  • Buhari: Najeriya Zata Goyi Bayan Rage Yawan Man Da OPEC Take Haka

Shugaba Muhammadu Buhari na tarayyar Najeriya ya bayyana cewa gwamnatinsa zata goyi bayan duk wani shiri na kasashe masu arzikin man Fetur ta OPEC zata yi na rage yawan man da zata haka saboda kyautata farashinsa a kasuwannin duniya.

Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto shugaban yana fadar haka ta bakin mai bashi shawara kan lamuran yada labarai da hulda da jama'a Malam Shehu Garba a jiya Laraba. 

Shehu garba ya ce shugaba Buhari ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da karamin ministan mai kula da al'amuran Afrika kuma jakadan Sarki Salman bin Abdul azizi na musamman Ahmad Qattan a fadar shugaban kasa a Abuja.

Shugaba Buhari ya kara da cewa Najeriya kasa ce wacce take mutunta kungiyar kasashe masu arzikin man Fetur ta OPEC don haka zata bada hadin kai a duk lokacinda ta bukaci a rage yawan man da ake haka don kyautata farashin a kasuwannin duniya. 

Shugaban ya kara da cewa, duk da cewa najeriya tana bukatar kudade don irin matsalolin da take fama da su wadanda suka hada da fadin kasa, rashin ci gaba da kuma yawan mutane. 

Daga karshe shugaban ya yi alkawali zasu tattauna batun da ministan man fetur na kasa don daukan matakin da ya dace.