Jam'iyya Ummah Ta Zargi Gwamnatin Sudan Shirin Kisan Kiyashi A Kasar.
(last modified Thu, 21 Feb 2019 06:51:43 GMT )
Feb 21, 2019 06:51 UTC
  • Jam'iyya Ummah Ta Zargi Gwamnatin Sudan Shirin Kisan Kiyashi A Kasar.

Majiyar jam'iyyar Umma, babbar jam'iyyar adawa a kasar Sudan ta bayyana cewa kashedin da gwamnatin shugaba Bashir ta bayar na murkushe yan adawa da karfi ya nuna cewa zata yi kisan kiyashi wa mutanen kasar.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya ce jam'iyyar ta bayyana haka ne a jiya Laraba bayan da gwamnatin ta fidda sanarwan cewa zata dauki matakin ba sani ba sabo kan dukkan yan adawan kasar wadanda suke zanga-zangar son ganin bayan gwamnatin shugaba Umar Hassan Albashir.

Tun ranar 19 ga watan Decemban da ya gabata ne mutanen kasar Sudan suke zanga-zangar neman ficewar gwamnatin shugaban Umar Hassan Albashir daga harkokin iko a kasar don gazawarta wajen biyan bukatun mutanen kasar, da kuma barin kayakin bukatun yau da kullum su fi karfin talaka. 

Ya zuwa yanzu dai majiyar gwamnatin kasar ta Sudan ta bayyana cewa mutane 30 ne suka rasa rayuansu sanadiyyar dirar mikiyan da jami'an tsaron kasar suke masu, amma majiyar kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu ya fi 40