Ana Zaben shugaban Kasa A Tarayyar Najeriya
A yau Asabar 23 ga watan Febreru da muke ciki ne ake gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisar dokoki na wakilai da dattawa.
Jaridar Premium times ta Nigeriya ta bayyana cewa mutane Najeriya wadanda suka cancanci zabe fiye da miliyon 70 ne ake saran zasu zabi shugaban kasa a cikin yan takarar neman wannan kujerar su 73. Fitattu daga cikinsu su ne shugaba mai ci Muhamadu Buhari na jam'iyyar APC da kuma Atiku A bubakar na jam'iyyar APC.
A bangaren majalisar dattawa kuma akwai kujeru 109 da za'a cike, da kuma kujeru 360 na majalisar wakilai. Wannan dai shi ne zabe na farko wanda gwamnati mai ci zata gudanar . Sai kuma a ranar 9 marche ne za'a gudanar da zaben gwamnoni da kuma majalisun jihohi.