An Fara Kidayar Kuri'u A Wasu Sassan Najeriya
Rahotanni daga Najeriya, na cewa an fara kidayar kuri'un babban zaben kasar da aka kada kuri'arsa yau Asabar.
Bayanai sun ce tuni aka fara fitar da sakamakon zaben a wasu sassan kasar, karkashin sanya idon jami'an tsaro.
A mafi akasari dai an ce an gudanar da zaben cikin lumana, saidai abunda ba a rasa ba, kamar hare haren rokoki da ake zargin mayakan boko haram da kaiwa a birnin Maiduguri dake arewa maso gabashin kasar gabanin kada kuri'a a zaben.
Ko baya ga hakan rahotanni sun ce an bude runfunan zabe cikin lokaci, inda kuma jama'a suka kada kuriar cikin kwanciyar hankali.
A inda kuma aka fuskanci tsaiko wajen fara zaben an kara lokaci, kamar yadda hukumar zaben kasar ta sanar.
Dukkan manyan 'yan takara a zaben da suka hada da shugaban Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC da babban abokin hamayyarsa Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP sun kada kuri’unsu a zaben shugabancin kasar da na ‘yan majalisun dattijai da na wakilai a yau Asabar.
Shugaba Buhari ya kada kuri’arsa ce da misalin karfe 8 na safiyar wannan Asabar a mahaifarsa garin Daura da ke jihar Katsina, yayinda babban abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar, ya kada tasa kuri’ar a Jada da ke jihar Adamawa da misalin karfe 10.
'Yan takara 73 ke neman darewa kujerar shugabancin najeriyar, kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.