Ana Ci Gaba Da Fitar Da Sakamakon Zabe A Najeriya
Rahotanni da suke fitowa daga Najeriya na nuni da cewa; An fara kidaya kuri’a a cibiyoyoyin zabe na sassa daban-daban na kasar.
A mazabar Garki da take a cikin babban birnin kasar ta Najeriya Abuja, an rufe kada kuri’a da misalin karfe 2.30 kamar yadda jaridar Vanguard ta kasar ta nakalto, sannan kuma an fara kidaya kuri’un da aka kada.
Bugu da kari, rahotannin da suke fitowa daga sassa daban-daban na kasar suna nuni da yadda aka yi zaben ba tare da wata matsala a mafi yawancin mazabu.
Bugu da kari an sanmi fitowar dandazon mutane masu kada kuri’a tare da yin dogayen layi a mazabu daban-daban.
A yankin arewa maso gabashin kasar ne aka sami rahotannin da suke Magana akan hare-haren kungiyar Boko-haram musamman a cikin birnen Maiduguri da kuma wasu yankuna na jahar Yobe.
A Jahohin Rivers da Lagos an sami rahotannin da su ka ambaci samun hatsaniya wacce ta kai ga lalata wasu akwatunan zaben.
Muhimman ‘yan takarar da suke gogayya da juna su ne Shugaba Muhammadu Buhari mai ci daga jam’iyyar APC sai kuma Alhaji Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP.