Sudan : EL-Bashir Ya Nada Sabon Mataimakinsa
(last modified Sun, 24 Feb 2019 09:32:11 GMT )
Feb 24, 2019 09:32 UTC
  • Sudan : EL-Bashir Ya Nada Sabon Mataimakinsa

Shugaban kasar Sudan Umar Hassan al-Bashir ya nada ministan tsaro a matsayin mataimakin shugaban kasa

Shugaban kasar na Sudan ya nada Awad Muhammad Ahmed Ibn Auf a matsayin mataimakin shugaban kasar, yayin da zai ci gaba da rike mukaminsa na ministan tsaro.

Shugaban kasar ta Sudan ya kuma kafa dokar ta baci har ta tsawon shekara guda a fadin kasar baki daya.

Matakan na shugaban kasar ta Sudan ya biyo bayan Zanga-zangar da al’ummar kasar suke yi na tsawon watanni biyu.

Zanga-zangar ta fara ne a cikin watan Disamba na shekarar da ta gabata  domin nuna kin amincewa da hauhawar farashin kayan abinci. Sai dai al’ummar kasar sun rika yin kira ga shugaba Umar Hassan al-Bashir da ya yi murabus daga kan mukaminsa.