Sakamakon Zabe A Tarayyar Najeriya Na Ci Gaba Da Fitowa
(last modified Mon, 25 Feb 2019 05:38:41 GMT )
Feb 25, 2019 05:38 UTC
  • Sakamakon Zabe A Tarayyar Najeriya Na Ci Gaba Da Fitowa

Sakamakon zaben shugaban kasa da majalisun dokokin tarayyar Najriya wanda aka gudanar a jiya Asabar suna ci gaba da fitowa.

Kamfanin dillancin Najeriya NAN ya bayyana cewa dan takara shugaban kasa na jam'iyyar APC dan Muhammadu Buhari ya kada dan takarar jam'iyyar  PDP Atiku Abubakar a rumfan zaben da ya kara kuri'arsa a jihar Adamawa. 

Sakamakon zabe a mazabar Ajiya 02 Gwabawa Yola Noth ya nuna cewa Atiku ya sami kuri'u 167 a yayinda Buhari ya samu 186 daga cikin kuri'u 365 da aka kada a mazabar.

Amma mazabar da buhari ya kada kuri'arsa wato Kofar Baru 3, a unguwar sarkin yari cikin karamar hukumar Daura na jihar Katsina, Buhari yana da kuri'u 523, a yayinsa Atiku na jam'iyyar PDP yake da kuri'u 3.

Sai kuma a jihar Lagos inda Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya ci zabe a mazabar da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbanjo yaka ku'ri'arsa. Tsohon mataimakin shugaban kasan ya sami kuriu 425 sannan jam'iyyar APC kuma ta sami kuri'u 229.