Najeriya : Buhari Ke kan Gaba A Zaben Shugaban Kasa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35370-najeriya_buhari_ke_kan_gaba_a_zaben_shugaban_kasa
Sakamakon zaben da aka sanar a jiya Litinin yana nuni da cewa; Shugaba Buhari ya samu nasara a jahohin Osun, Kogi, Gombe, Eikiti, Nasarawa, Yobe, da Kwara. Shi kuwa dan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Atuku Abubakar ya sami nasara ne a cikin babban birnin tarayyar kasar Abuja, sai jahohin Ebonyi, Ondo, Abia da Enugu.
(last modified 2019-04-27T14:25:10+00:00 )
Feb 26, 2019 06:07 UTC
  • Najeriya : Buhari Ke kan Gaba A Zaben Shugaban Kasa

Sakamakon zaben da aka sanar a jiya Litinin yana nuni da cewa; Shugaba Buhari ya samu nasara a jahohin Osun, Kogi, Gombe, Eikiti, Nasarawa, Yobe, da Kwara. Shi kuwa dan takarar jam’iyyar PDP Alhaji Atuku Abubakar ya sami nasara ne a cikin babban birnin tarayyar kasar Abuja, sai jahohin Ebonyi, Ondo, Abia da Enugu.

Turawan zabe na kowace jaha ne su ka rika gabatar da sakamakon zaben jahohin nasu a babbar cibiyar hukumar zabe mai zaman kanta a babban birnin tarayya Abuja.

Sai dai jam’iyyar PDP ta yi koken cewa da akwai almundahana a cikin yadda ake sanar da sakamakon zaben.

 Ana sa ran cigaba da sanar da sakamakon zaben  a yau Talata da zai iya ba da haske akan wanda ya lashe shi.