Gabon : Ali Bongo Ya Koma Gida
(last modified Tue, 26 Feb 2019 06:12:33 GMT )
Feb 26, 2019 06:12 UTC
  • Gabon : Ali Bongo Ya Koma Gida

Ana ci gaba da samun sabani akan halin lafiyar shugaban kasar ta Gabon wanda ya dade yana jiyya a kasar Moroko

Majiyar gwamnatin kasar ta Gabon ta ce; Shugaban ya koma gida kuma ya gana da manyan jami’an gwamnati da ‘yan majalisa.

Wani jami’in gwamnatin kasar ta Gabon ya shaida wa manema labaru cewa ya zuwa yanzu babu cikakken bayani akan ko ya dawo kenan baki daya ko kuma zai sake komawa asibiti.

Rashin samun cikakken bayani akan halin lafiyar shugaban kasar ya karu a cikin watan janairu da wasu sojojin kasar su ka jagoranci juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Ali Bongo ya zama shugaban kasar Gabon ne bayan mutuwar mahaifinsa Umar Bongo wanda ya rasu a 2009. An sake zabarsa shugaban kasa a 2016.