Najeriya : Buhari Ya Sake Lashe Zaben Shugaban Kasa
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya ta sanar da sakamakon zaben shugaban kasar wanda ya bayyana Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben a karo na biyu.
Sakamakon ya nuna cewa shugaba Buhari na Jam'iyyar APC ya samu kuri'u 15,191,847, yayin da babban abokin hamayarsa na Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya samu kuri'u 11,262,978, kamar yadda shugaban hukumar Zabe ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana a cikin daren jiya.
Wannan nasara dai zata baiwa shugaba Buhari mai shekaru 76, damar sake mulkar kasar na karin shekaru hudu masu zuwa.
Sakamakon ya kuma nuna shugaba Buhari ya samu nasara a jihohi 19 daga cikin 36 na kasar, yayin da Alh, Atiku Abubakar ya samu jihohi 17 da kuma babban birnin kasar Abuja.
Sai dai jam'iyyar adawa ta PDP, ta yi watsi da sakamakon zaben da Hukumar ta INEC ta fitar.
Kafin dai wani dan takara ya lashe zaben shugaban kasa a Najeriya, tun zagaye na farko, to sai ya zamana bayan rinjayen da yake dashi, ya samu kuma kashi 25% na yawan kuri'un da aka kada a cikin kashi biyu cikin uku na jihohin kasar 36 ciki harda babban birnin Abuja.
A wani lokaci nan gaba ne ake sa ran shugaban kasar zai yi jawabin murna ga magoya bayansa.