Najeriya: Atiku Ya Gabatar Da Tawagar Lauyoyinsa Dominn Kalubalantar Sakamakon Zabe
Dantakar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a tarayyar Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya gabatar da tawagar lauyoyinsa wadanda zasu kalubalanci zaben da aka yi wa shugaban Buhari a zaben ranar Asabar da ta gabata
Jaridar Premiums Times ta Najeriya ya kara da cewa Babban lauya Livy Uzoukwu ne zai shugabancin tawagar lauyoyin wadanda zasu gabatar da kara a gabam kotu su gaba ci gada da kare matsayinsu har zuwa karshen shari'ar.
Atiku Abubakar dai ya yi watsi da sakamakon zaben na ranar Asabar da ta gabata, inda yake zargin gwamnati mai ci da amfani da sojoji da kuma jami'an tsaro don murda sakamakon zabe a wuraren da jam'iyarsa ta PDP take da karfi. Banda haka Atiku yana zargin hukumar zabe mai zaman kanta da hannu wajen murda zaben na ranar asabar wanda ya kai ga nasarar shugaba Muhammadu Buhari.
Duk kokarinda komitin zaman lafiya karkashin tsohon shugaban kasa Abdussalam Abubakar ya yi na hana dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na ya bar batun zuwa kotu bai sami nasara ba.