Sudan: Shugaban Yan Adawa Ya Bukaci Shugaba Albashir Ya Sauka
(last modified Sun, 03 Mar 2019 07:34:57 GMT )
Mar 03, 2019 07:34 UTC
  • Sudan: Shugaban Yan Adawa Ya Bukaci Shugaba Albashir Ya Sauka

Shugaban jam'iyyar Umma, jam'iyyar adawa mafi girma a kasar Sudan ya bukaci shugaba Umar Hassan Albashir ya sauka da mukaminsa

Majiyar muryar JMI ta kara da cewa Sadiqul Mahdi ya bayyana haka ne a jiya Abar da dare, ya kuma kara da cewa yakamata shugaban ya fara tattaunawa da yan adawa don kafa gwamnatin rikon kwarya. 

Shugaban yan adawar ya fadi haka ne a dai-dai lokacinsa shugaba Umar Hassan Albashir yake daukar matakai daya bayan daya don fuskantar kalubalan da yake barazana ga shugabancin sa. 

Daga cikin matakan da shugaban ya dauka dai akwai rusa gwamnatin kasar, sauya dukkan gwamnonin lardunan kasar, da kuma shelanta halin ko ta kwana a duk fadin kasar. 

Tun ranar 19 ga watanDecemban da ya gabata ne mutanen kasar Sudan a duk fadin kasar suke zanga-zanga a duk fadin kasar don neman shugaba Umar Albashir ya sauka daga kujerar shugabancin kasar bayan ya kasa biyan bukatun rayuwar mutane na yau da kullum.