D.R Congo : Tshisekedi Ya Yi Alkawarin Sakin Fursunonin Siyasa
Shugaba, Félix Tshisekedi, na Congo, ya bayyana aniyarsa ta sakin dukkan fursunonin siyasa da ake tsare dasu a kasar.
Shugaban ya bayyana cewa nan gaba zai bukaci mai'aikatar shari'a ta kasarsa data sallami dukkan fursunonin siyasa da ake tsare da saboda sabanin ra'ayi, musamman wadanda aka cafke a yayin boren kasar na gabanin zabe.
Mista Tshisekedi, ya bayyana hakan ne a cikin wani jawabin da ya gabatar kan tsarinsa na gaggawa da yake fatan aiwatarwa a cikin kwanaki dari na kama mulkinsa.
Haka kuma shugaban ya ce zai yi kokarin ganin 'yan kasar ta Congo dake gudun hijira a kasashen waje saboda dalilai na siyasa sun dawo gida.
Masana dai na ganin sakin fursunonin siyasa a kasar ta DR Congo, zai kawo karshen irin salon siyasar tsohon shugaban kasar Joseph Kabila, wanda gwamnatinsa ta jima tana harmata zanga zanga ta 'yan adawa.
A wannan kasa ta Jamhuriya Demukuradiyyar Congo, akwai 'yan adawa da ake tsare da ko kuma suke gudun hijira a tsawan shekaru 18 na mulkin shugaba J. Kabila, ko baya ga hakan kuma akwai 'yan adawa da dama da aka kashe a lokacin boren kin jinin anniyar tsohon shugaban kasar na mika mulki bayan karshen wa'adin mulkinsa a karshen shekara 2016.