Najeriya ta sabawa ka'ida wajen mika jagororin 'yan awaren Kamaru
(last modified Mon, 04 Mar 2019 05:03:44 GMT )
Mar 04, 2019 05:03 UTC
  • Najeriya ta sabawa ka'ida wajen mika jagororin 'yan awaren Kamaru

Wata Kotu a Najeriya ta bayyana cewa mika jagororin ‘yan aware na Kamaru ga hukumomin kasar ya sabawa shari’a, da ma kundin tsarin mulkin kasar.

Kotun ta yi la’akari da yadda mutanen suka nemi mafaka, kuma aka basu a tarayya ta Najeriya kafin a mikasu ga gwamnatin kasarsu.

A watan Janairun shekara data gabata ne mahukuntan Najeriyar suka mika jagororin ‘yan a ware a yankin masu amfani da turancin Ingilishi na kamaru su 47, da suka tsere zuwa Najeriyar ga gwamnatin kasar Kamaru bayan rikicin yankin ya tsananta.

Hukumar kula da ‘yan gudun hjira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce galibin mutanen 47 sun nemi mafaka kuma an basu a Najeriyar amma kuma lokaci guda aka mika su ga gwamnatin Kamaru don fuskantar hukunci, duk da cewa an basu mafaka a najeriyar.