Afrika Ta Tsakiya : Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ta Fara Gamuwa Da Cikas
(last modified Mon, 04 Mar 2019 13:37:00 GMT )
Mar 04, 2019 13:37 UTC
  • Afrika Ta Tsakiya : Yarjejeniyar Zaman Lafiya Ta Fara Gamuwa Da Cikas

Wani gungun 'yan tawaye daga cikin 14 da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya, ya sanar da janyewarsa daga yarjejeniyar.

Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da gwamnatin kasar ta Afrika ta tsakiya, ta sanar da kafa sabuwar gwamnati, wacce tunda farko ma wani gungun masu dauke da makamai ya kalubalanta.

Gungun 'yan tawayen na (FPDC), ya kudiri anniyar janye wa daga yarjejeniyar ba tare da wata wata ba, saboda a cewarsa gwamnatin da aka kafa ta sabawa yarjejeniyar da aka cimma a birnin Khartoum.

Dama kafin hakan a jiya Lahadi, wani gungun 'yan tawayen mai dauke da makamai mai suna FPRC, ya yi fatali da yarjejeniyar, tare da shan alwashin janyewa daga gwamnatin.

yarjejeniyar da aka cimma a Kahrtoum, aka kuma daddale a Bnagui babban birnin kasar a ranar 6 ga watan Fabarairu da ya gabata, ta tanadi kafa gwamnatin hadin kai data tanadi baiwa gungun 'yan tawayen mukami a gwamnatin, saidai ba'a samu wani sauyi na-azo-a-gani-ba, inda gungun 'yan tawaye shida ne cikin 14 suka samu mukami a majalisar ministocin kasar.