Ministocin Kudin Afrika Na Taro A Kamaru
(last modified Wed, 06 Mar 2019 05:50:19 GMT )
Mar 06, 2019 05:50 UTC
  • Ministocin Kudin Afrika Na Taro A Kamaru

Ministocin kudi da kwararru na kasashen Afrika na gudanar da wani taron kwanaki biyar a Yaounde, babban birnin jamhuriyar Kamaru, domin nazarin hanyoyi da matakan da za'a dauka don bunkasa ci gaban nahiyar.

Taron wanda aka fara ranar Litini, ya hada dukkannin mambobin kasashen dake kungiyar tarayyar Afrika da suka hallara a Kamaru domin tattauna yadda za a lalubo bakin bakin zaren warware matsalolin, da kuma yadda za a ciyar da tattalin arzikin nahiyar gaba.

Taron wanda kwamitin kwararru na musamman na kungiyar tarayyar Afrika da ya shafi batun kudi da tsare tsaren tattalin arziki  wato STC ya shirya tare da hadin gwiwar gwamnatin Kamarun, na da gurin kawo sauye sauye a tsarin tattalin arziki.

Ministan kudin jamhuriyar Kamaru, Louis Paul Motaze, wanda ya jagoranci bude taron ya ce "A Kamaru muna da tunanin kawo sauye sauye ga tsarin tattalin arziki, saboda shi ne zai haifar da ci gaban albarkatun kasarmu, tare da samar da guraben ayyukan yi, musamman ga matasa, don haka a cewarsa wannan taro yana da matukar muhimmanci.