Najeriya : Ana Daf Da Kada Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da 'Yan Majalisun Jiha
(last modified 2019-03-09T03:57:08+00:00 )
Mar 09, 2019 03:57 UTC
  • Najeriya : Ana Daf Da Kada Kuri'a A Zaben Gwamnoni Da 'Yan Majalisun Jiha

A Najeriya, yau ne al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben 'yan zaben gwamnoni da 'yan majalisun jihohi.

Za'a gudanar da zaben gwamnoni ne a cikin jihohi 29 daga cikin 36, kasancewar akwai jihohi 7 da ba za su yi zaben gwamna ba saboda gwamnoninsu ba su kammala wa'adinsu ba, amma zaben 'yan majalisun johohin za'a gudanar dashi a duk fadin kasar.

'Yan aksar kimanin miliyan 72 ne aka kiyasta zasu kada kuri'a a zaben na yau Asabar.

Zaben dai na zune ne bayan nasara da shugaban kasar Muhamadu Buhari ya samu a zaben shugaban kasar da ya gudana a watan jiya inda ya doke abokin hamayarsa na njam'iyyar PDP, Alh. Atiku Abubakar, da kashi 56% na yawan kuri'un da aka kada, sakamakon da jam'iyyar ta PDP ta fatali dashi bisa zargin cewa an tafka magudi.

Zaben na yau dai zai yi zafi sosai, a wasu jihiohin kasar.

Tun a zaben shekara 2015 dai Jam'iyyar APC, ke rike da iko a jihohi 23 na kasar, a yayin da PDP ke rike da jihohi 13.

Tags