Mar 09, 2019 14:47 UTC
  • Ana Gudanar Da Zaben Gwamnoni Da 'Yan Majalisun Jihohi A Nijeriya

A Nijeriya a yau Asabar ‘yan kasar na ci gaba da kada kuri’a a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi a mafi yawa daga cikin jihohin kasar, makwanni biyu bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar, don zaban gwamnoni da 'yan majalisun jihohi na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Tun da safiyar yau ne dai miliyoyin al'ummar kasar suka fito don kada kuri'unsu ga 'yan takarar da suke so a zaben da ake ganin zai yi zafi musamman a wasu jihohi na kasar inda ake sa ran wasu gwamnoni masu ci za su fuskantar gagarumin kalubale a kokarin da suke yi na ci gaba da mulki.

Hukumar zaben kasar INEC ta bayyana cewar za'a a gudanar da zaben gwamna din ne a jihohi 29 cikin 36 na kasar inda sauran jihohi 7 din kuma da suka hada da Kogi, Osun, Ondo, Anambra, Ekiti da kuma Edo sai a wani lokaci a nan gaba za a gudanar da zaben.

A matakin 'yan majalisun jihohi kuma, za a zabi 'yan majalisu guda 991 cikin 'yan takara 14, 583 da za su fafata a jihohi 36 na kasar.

Shugaban kasar Muhammadu Buhari dai ya kada kuri'arsa ne a mazabarsa ta Kofar Baru polling unit a garin Daura, da ke jihar Katsina. Kafin hakan dai ya kirayi al'ummar kasar da su fito su kada kuri'unsu cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A halin yanzu dai jam'iyyar APC mai mulki a kasar ita ce take kan gaba wajen yawan gwamnoni a kasar inda take da gwamnoni 22, sai kuma jam'iyyar PDP mai biye mata da gwamnoni 13 sai kuma jam'iyyar AFGA mai gwamna guda.

 

Tags