Ana Zaben 'Yan Majalisar Dokoki A Guinea Bissau
Yau Lahadi, al'umma a Guinea Bissau na kada kuri'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar, wanda ake fatan zai kawo karshen rikicin siyasar da kasar ke fama dashi.
Jam'iyyun siyasa 21 ne ke fafatawa a zaben, domin samun wakilcin jama'a a majalisar dokokin kasar data kunshi kujeru 102.
Bayanai sun nuna cewa a wannan karo an samu takarar mata dayewa wanda ya kai kashi 36 cikin dari na 'yan takaran.
Nan da sa'o'i 48 ne ake sa ran fara fitar da sakamakon zaben.
Rikicin siyasa ya dai barke ne a Guinea Bissau, a cikin shekara 2015, bayan da shugaban kasar , José Mario Vaz, ya kori Pira ministansa, Domingos Simoes Pereira, wanda shi ne shugaban jam'iyyar (PAIGC), dake shugancin kasar tun bayan samun 'yancin kai a 1974.