D.R Congo : Tshisekedi Ya Yi Wa Fursunonin Siyasa 700 Afuwa
Shugagba Félix Tshisekedi, na Jamhuriya Demokuradiyyar Congo ya yi afuwa wa fursunonin siyasa 700 na kasar.
A cikin sanarwar da aka karanto a cikin gidan talabijin din aksar, shugaba Tshisekedi, ya kuma ce nan gaba ma za'a saki wasu fursunonin siyasar 700.
Daga cikin wadanda akayi wa afuwar harda wani jigon 'yan adawa na kasar Franck Diongo, da kuma wasi lauya da aka yankewa hukuncin daurin rai da rai a shekara 2009.
A kwanan baya ne shugaban kasar ta D R Congo, ya bayyana aniyarsa ta sakin dukkan fursunonin siyasa da ake tsare dasu a kasar.
A wannan kasa ta Jamhuriya Demukuradiyyar Congo, akwai 'yan adawa da ake tsare da ko kuma suke gudun hijira a tsawan shekaru 18 na mulkin shugaba J. Kabila, ko baya ga hakan kuma akwai 'yan adawa da dama da aka kashe a lokacin boren kin jinin anniyar tsohon shugaban kasar na mika mulki bayan karshen wa'adin mulkinsa a karshen shekara 2016.