Mar 15, 2019 08:50 UTC
  • An Bude Taron Kasa Da Kasa Na Raya Afrika A Morocco

An bude taron kasa da kasa karo na 6, kan raya nahiyar Afrika, a birnin Casablanca na kasar Morocco.

Taron na yini biyu da aka fara jiya Alhamis, wanda kuma asusun zuba jari na Morocco ''Al Mada'' ya shirya, dandali ne na tattaunawa da inganta zuba jari da cinikayya tsakanin kasashen nahiyar

Shugaban kasar Saliyo, Julius Maada Bio da kasarsa ke matsayin babbar bakuwa ne ya jagoranci bude taron mai taken "when East meets West" wato "a lokacin da gabas ta hadu da yamma".

Da yake jawabi, shugaban na Saliyo, ya jadadda cewa Afrika na da dimbin damarmaki da yawan al'ummarta da ya kai biliyan daya da kuma albarkatu daban-daban da take da su, sai dai kuma ba a amfani da wadananan dimbin albarkatu.

Ya kara da cewa, nahiyar na da damarmaki da dama ga masu zuba jari a fannoni daban-daban kamar aikin gona da cinikayya da makamashi mai tsafta.

Shugaba Maada Bio, ya jaddada bukatar shawo kan manyan kalubalen inganta zaman lafiya da yaki da cin hanci.

Tags