Mar 16, 2019 05:19 UTC
  • An Kashe 'Yan Ta'adda Da Dama A Najeriya

Dakarun Tsaron Najeriya Sun Sanar da Hallaka 'yan ta'addar ISIS 33

Kafanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Dakarun tsaron Najeriya na cewa Kungiyar IS  ta kai wa rundunar sojin Najeriya hari a arewa maso gabashin kasar.

Sai dai rundunar sojin Najeriyar ta ce dakarun hadin gwiwa sun fafata da mayakan kungiyar, kuma sun kashe 'yan bindigar 33 tare da kwace makamai da motoci.

A wata sanarwa, kungiyar IS din ta ce dan kunar bakin wake a cikin wata mota ne ya kai hari kan wani gungun sojoji a garin Arege kusa da tafkin Chadi.

Harin na kunar bakin wake dai ba a saba ganin kungiyar na kai irinsa ba, ganin ta fi amfani da bindigogi ko kuma abubuwan fashewa wajen kai wa rundunar sojin Najeriya hari.

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da aiki da rundunonin kasa da na sama daga Kamaru da Nijar don yaki da masu tayar da kayar bayan.

A watan jiya ne kungiyar masu ikirarin jihadi suka kai hare-hare a jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, a wani tunkuri na tarwatsa zabukan da aka gudanar a kasar.

Tags