Mar 16, 2019 13:22 UTC
  • Gambia : Shugaba Barrow, Ya Kori Mataimakinsa

Shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, ya kori mataimakinsa Ousainou Darboe, daga bakin aiki.

Sanarwar da aka karanto a gidan talabijin din kasar, bata bayyana takamaimai lafinda ake zargin mataimakin shugaban kasar ba.

Ko baya ga mataimakinsa, shugaban kasar yakuma  kori ministocin kasuwanci dana aikin gona na kasar.

An dai maye gurbin mataimakin shugaban kasar da ministan lafiya na kasar Isatou Touray.

Bayanai daga kasar sun ce an kori mataimakin shugaban kasar ne saboda sabanin da da ya kunno kai tsakanin  shugaba Barrow da kuma jam'iyyar UDP, wacce karkashinta ne shugaban ya kayar da tsohon shugaban kasar Yahyah Jammeh a zaben kasar na watan Disamban 2016.

Wasu rahotanni na daban sun ce an fuskantar takun tsaka ne tsakanin jam'iyyar ta UDP, da kuma shugaban kasar, wanda ke son yin afani da wani bangarenta na matasan jam'iiyar domin sake tsayawa takara nan gaba.

Tags