Mar 21, 2019 15:04 UTC
  • Mutane 200,000 Ke Bukatar Tallafi Bayan Iftila'i A Zimbabwe

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, mutane 200,000 ne ke bukatar tallafi bayan iftila'in mahaukaciyar guguwar nan mai hade da ambaliyar ruwa ta Idai data aukawa kasar Zimbabwe.

Tunda farko dai an bayyana cewa mutane kimanin 15,000 ne suka rasa muhallansu, saidia a cewar kakakin hukumar kula da abinci ta MDD, (WFP ko PAM), Hervé Verhoosel, adadin mutanen dake bukatar dauki ya karu matuka bayan bincikar lamarin.

Jami'in ya kara da cewa al'amura sun dagule sosai a lardin Chimanimani, dake gabashin kasar Zimbabwe, Wanda a cewarsa kashi 90% na lardin ya lalace sosai.

A wani labari kuma gidan talabijin din kasar, ya ce adadin mutanen da suka rasa rayukansu a ifti'la'in ya kai 139.

A cikin daren ranar 15 ga watan Maris din nan ne zuwa 16 mahaukaciyar Gugumar mai hade da ruwan sama da ake wa lakabi da Idai data haifar da ambaliya, ta aukawa kasashen Mozanbik, da Malawi da kuma gabashin Zimbabwe.

Tags