An Sake Zaben Isma'il Omar Guelleh A Matsayin Shugaban Jibouti
Rahotanni daga kasar Jibouti sun ce shugaban kasar Isma'il Omar Guelleh shi ne ya sake lashe zaben shugaban kasar.
A wata sanarwa da Firaministan kasar at Jibouti Abdulkadir Kamal Muhmamd ya bayar ya sheda cewa, shugaba Isma'il Omar Guelleh ne ya sake lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar, a wani sabon wa'adin mulki na shekaru 5.
Guelleh ya lashe zaben da babban rinjaye, bayan da mafi yawan jam'iyyun adawa akasar suka kaurace ma zaben.
Tun a cikin shekara ta 1999 ce dai Isma'il Omar Guelleh yake kan kujerar shugabancin kasar Jibouti, kuma a cikin shekara ta 2010 ya yi wa kundin tsarin mulkin kasar garanbawul, inda ya sauya dokar da ta kayyade shugabancin kasar a cikin shekaru 10 kawai a wa'adin mulki guda biyu.