Zimbabuwe : 'Yan Adawa Sun Kira Zanga-Zanga Saboda Talauci
-
Jagoran 'yan adawa a Zimbabuwe, Morgan Tsvangirai.
Babbar jam'iyyar adawa a kasar Zimbabuwe ta yi kiran wata gagarimar zanga-zanga gobe Alhamis domin yin allawadai da halin da tattalin arzikin kasar ya shiga.
Kanfanin dilanacin labaren APA ya rawaito jagoran Jam'iyyar ta (MDC) kana tsohon firaministan kasar Morgan Tsvangirai na bayana cewa babban abun damuwa ne kan yadda tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa ba.
'yan adawa dai a wannan kasar na zargin gwamnati da rashin tabaka komai, a yayin da dubban al'ummar kasar ke fama da matsanancin talauci.
"yan sanada dai
'Yan sanda dai sun haramta zanga-zanga.
kanfanoni da dama ne dai a kasar Zimbabuwe suka durkushe a tsawan shakarun baya bayan nan saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Kimanin 'yan kasar Zimbabuwe miliyan hudu ke fuskantar barazana yunwa da bukatar tallafin gaggawa saboda fari dake ci gaba da addabar kasar.