Somaliya : An Kai Harin Bom A Wata Kasuwa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3847-somaliya_an_kai_harin_bom_a_wata_kasuwa
Rahotanni daga Somaliya na cewa mutane uku ne suka rasa rayukan su, kana wasu shida na daban suka raunana sakamakon fashewar wani bom a cikin wata kasuwa dake kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:28:07+00:00 )
Apr 13, 2016 18:07 UTC
  • Somaliya : An Kai Harin Bom A Wata Kasuwa

Rahotanni daga Somaliya na cewa mutane uku ne suka rasa rayukan su, kana wasu shida na daban suka raunana sakamakon fashewar wani bom a cikin wata kasuwa dake kudancin kasar.

lamarin dai ya auku ne a lardin Afgoye dake nisan kilomita 30 daga yammacin Mogadisho babban birnin kasar a wata kasuwar sayar da dabbobi, kamar yadda wani jama'in tsaro mai suna Adbulkadir mohamed ya tabbatarwa da kanafanin dilancin labaren AFP.

Wani ganau ya shaidawa masu aiko da rahotanni cewa lamarin ya tsoratar da jama'a dake wurin sosai.

kawo yanzu dai babu wata kungiya data dau alhakin kai wannan harin, saidai so tarin yawa akan danganta ire-iren wadanan munannen ayyukan ga kungiyar nan ta Alshabab data yi kaurin suna wajen aikata ayyukan ta'adi a wannan kasa.

kungiyar ta Alshab dai ta sha alwashin cewa sai ta kawar da gwamnatin kasar ta Somaliya dake samun goyan bayan kasashen duniya da kuma dakarun wazar da zamen lafiya na kungiyar tarayya Afirka a Somiliya (Amisom) dake kunshe da dakaru 22,000.

-