Gwamnatin Kasar Ghana Ta Sanar Da Daukan Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar
(last modified Sat, 16 Apr 2016 17:07:39 GMT )
Apr 16, 2016 17:07 UTC
  • Gwamnatin Kasar Ghana Ta Sanar Da Daukan Tsauraran Matakan Tsaro A Kasar

Gwamnatin kasar Ghana ta sanar da daukar tsauraran matakan tsaro a kasar don kare kasar daga duk wani kokari na kai hare-haren ta'addanci tana mai kiran al'ummar kasar da su yi taka tsantsan ainun.

Kafar watsa labaran Africa Times ta bayyana cewar shugaban kasar Ghana John Dramani Mahamma ne ya sanar da hakan a yau Asabar inda ya ce gwamnati ta dau tsauraran matakan tsaro a duk fadin kasar don fada da duk wani kokari na kai harin ta'addanci a kasar yana mai kiran al'ummar kasar da su yi taka tsantsan da kuma zama cikin shirin ko ta kwana.

Rahotanni daga kasar Ghanan sun ce gwamnatin ta dau wannan matakin ne bayan da majalisar koli ta tsaron kasar ta bayyana cewar ta sami wasu karfafan dalilai da hujjoji da suke nuni da cewa kungiyoyin 'yan ta'adda da suke zaune a kasar Ivory Coast suna shirin kai wasu hare-haren ta'addanci a kasar ta Ghana.

A kwanakin baya ne dai wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da suke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida suka kai wasu hare-hare kasar Ivory Coast, Burkina Faso da kuma Mali lamarin da ya sanya kasashen yankin daukar matakan tsaro don kare afkuwar hakan a kasashensu.