Shugaban Kenya Ya Yi Kira Zuwa Ga Hadin Kan Kasarsa
Shugtaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta tare da mataimakinsa William Roto sun yi kira zuwa ga sulhu da yafiya a tsakanin al'ummar kasa baki daya.
Kamfanin dillanicn labaran AFP daga birnin Nagoru na kasar Kenya ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake halartar wani gangami na dubban magoya bayansa a wani makeken filin wasa da ke garin, shugaban kasar ta Kenya tare da mataimakinsa sun yi kira da babbar murya kan a manta da duk wani abu da zai iya kawo rarraba da rashin fahimtar juna a tsakanin a'ummar kasar.
A lokacin da yake magana kan batun rikicin da ya faru a kasar a cikin shekarun 2007 da 2008, Kenyatta ya bayyana takaicinsa matuka kan abubuwan da suka faru, inda ya ce abin bakin ciki ne, kuma yana fata wani mai kama da haka ba zai sake faruwa a kasar Kenya ba, tare da yin kira da a hada kai tare da yin sulhu a tsakanin dukkanin bangarori na al'ummar kasar domin ci gabanta da zaman lafiyarta.