Kungiyar Boko Haram ta kaiwa Barikin Sojin Najeria hari
Rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan dakarunta na bataliya ta 113 da ke garin Kareto a arewacin jihar Borno.
Kamfanin dillancin Labaran Reuteus ya nakalto kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani Kukasheka Usman, cikin wata sanarwa da ya aikewa manema labarai ya ce da jijjifin safiyar yau ne mayakan na boko haram suka kai harin ba zata kan Bataliyar soja ta 133 dake Kareto a arewacin jihar borno kuma dakarun na can suna fafatawa da mayakan Boko Haram.
Sai dai sanarwar ba ta yi karin bayani ba dangane da adadin mutanan da suka rasa rayukansu ko kuma suka jikkata ba.
A baya bayan nan dai dakarun sojin kasar na cewa suna samun galaba a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram, inda ma suke cewa yanzu kungiyar ba ta da wani karfi da za ta iya tunkarar sojojin na Najeria, amma yanzu sai gashi kwashan mayakan na boko haram sun kai wa barikin soja na bataliya 113 hari, wannan hari dai ya yi bazata ga Al'ummar kasar.
Tun a shekarar 2009 ne kungiyar ta boko haram ta fara kai hare-haren ta'addanci a Najerian, lamarin da ya yi sanadiyar salwanta rayukan mutane sama da dubu 20, yayin da ya raba wasu milyoyi na daban da mahalinsu.