Mayakan Kungiyar Al-Shabab Sun Kai Hari Birnin Mogadisho Fadar Mulkin Somaliya
Yan kungiyar Al-Shabab ta Somaliya sun kai wani hari birnin Mogadisho fadar mulkin kasar, inda suka kashe mutane akalla 4 tare da jikkata wasu wasu adadi na daban a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya watsa rahoton cewa; Mayakan kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabab sun kaddamar da wasu jerin hare-hare ta hanyar bude wutan bindiga da tarwatsa wata mota da suka makare da bama-bamai a birnin Mogadisho fadar mulkin kasar Somaliya lamarin da ya kai ga hasarar rayukan mutane akalla 4 tare da jikkata wasu adadi na daban.
Majiyar rundunar 'yan sandan kasar ta Somaliya a ta bakin wani babban jami'inta mai suna Nur Usman ta tabbatar da kai jerin hare-haren na jiya tare da fayyace cewa; Tarwatsewar motar da aka makare da bama-bamai bai kai ga hasarar rai ba, amma bude wuta kan mai uwa da wabi da 'yan ta'addan suka yi ne ya lashe rayukan mutane hudu tare da raunata wasu na daban.