Sudan : An Bamkawa Gidan Gwanan Darfur Wuta
Apr 19, 2016 06:26 UTC
Wasu 'yan bindiga a Sudan sun kai hari tare da kona fadar gwamnan jihar Darfour, a gabashin kasar a washe garin wani kazamin fada kabilancin a yankin.
'yan bindigan sun bude wuta ne a fadar inda sukayi arangama da jami'an gardi sarki, kafin daga bisani gidan ya kama da wuta.
Mutane akallah 20 ne aka tabbatar cewa sun mutu a rikicin kabilun labarawa Maaliya da Rizeigat daya barke bayan satar dabbobi.
Wasu mazauna yankin sun ce kabilun Rizeigat ne suka kai ma fadar gwamnan jihar harin domin daukan fansa, koda yake bisa ga dukkan alamu a cewar su gwamnan baya wurin a lokacin.
Tags