Tsagerun Niger-Delta Sun Barazanar Ci Gaba Da Tarwatsa Bututun Man Fetur
Wani gungu na tsagerun yankin Niger-Delta a Najeriya ya yi barazanar ci gaba da tarwatsa bututun mai da iskar gas a yankunan kudancin kasar.
Kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da suka fitar kuma suka saka a shafukansu na yanar gizo, tsagerun na Niger-Delta sun ce su ne suka kai munanan hare-hare kan bututun mai a cikin watan Fabrairu a yankin, wanda ya yi sanadiyyar dakatar da ayyukan kamfanin shell na tsawon makonni.
Bayanin nasu ya ce mahukuntan Najeriya sun nuna musu cewa danyen man fetur da ake fitarwa a yankunansu ne kawai ke da amfani da mhimmanci, ba rayukan al'mmomin yankin ba.
A cikin 'yan kwanakin nan shugaba Buhari ya yi kashedin cewa zai shiga kafar wando daya da tsagerun na Niger-Delta da suke dauke da makamai suna fasa bututun, kamar yadda ya shiga kafar wando daya da Boko haram, yayin da mataimakin shgaban kasar Prof. Yemi Osinbajo ya ce, ayyukan fasa bututun na jawo wa Najeriya hasa ta ganga 250,000 ta mai a kowace rana.