An cimma yarjejjeniya kan fitar Dakarun MDD daga Yankin Darfur na Sudan
Gwamnatin Sudan, Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Afirka sun cimma matsaya kan fitar da dakarun su daga yankin Darfur na yammacin kasar Sudan.
Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa daga birnin Khartum ya nakalto Ali Assidik mai magana da yawun Ma'aikatar harakokin wajen Sudan na cewa bayan zaman da wakilan Gwamnati, MDD da Kungiyar Tarayyar Afirka suka yi sun cimma matsaya na janye Dakarun kungiyoyin daga yankin Darfur, kuma a ranar 8 ga watan Mayu mai kamawa bangarorin za su gudana da wani zama domin diba yadda za a janye dakarun da kadan kadan.
Kakakin Ma'aikatar harakokin wajen na kasar Sudan ya bayyana cewa kasar Sudan na fatan cewa a rahoto na gaba Majalisar Dinkin Duniya za ta bayyana irin ci gaba tare da konciyar hankalin da aka samu gami da karshen 'yan tawaye a yankin Darfur.