Boko Haram ta yi wa mataimakin kwamandan Soji kwanton-bauna
Mayakan Boko Haram sun kai hari a kan ayarin motar wani mataimakin kwamandan sojoji mai suna janar Victor Ezugwu dake kan hanyarsa ta kai ziyara a sansanin soji na garin Bama dake jahar Borno.
Kakakin Rundunar sojin kasa, Kanal Sani Usman Kukasheka, ya tabbatar da mutuwar Soji guda da kuma jikkatar wasu sojoji 2 daga cikin ayarin tawagar sojan dake maramasa baya, sai dai ya ce sojojin sun ci karfin mayakan inda suka yi nasarar kashe wasu daga cikinsu tare da karbe wasu makamai da mota guda kirar Hilux.
Wannan harin dai bai hana Janar Ezugwu kai ziyarar garin na Bama ba,a bangare guda kuma an mayar da gawar sojin daya mutu da sauran wadanda suka ji rauni garin Maiduguri.
Kanar kukasheka ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba, har sai sun ga karshen kungiyar Boko Haram.
Harin na jiya talata na zuwa ne kwana guda kacal bayan harin da 'yan kungiyar boko haram suka kaiwa barikicin Soja na bataliya 113 dake garin Kareto dake arewacin jahar Borno.