Yerjejeniyar Sulhu Ta Sudan Ta Kudu Tana Faskantar Barazanar Rushewa
Gwamnatin sudan ta kudu da kuma bangaren yan tawaye suna zargin juna kan rashin dawowar mataimakin shugaban kasa Riek
Gwamnatin sudan ta kudu da kuma bangaren yan tawaye suna zargin juna kan rashin dawowar mataimakin shugaban kasa Riek Machar zuwa birnin Juba babban birnin kasar don kafa gwamnatin hadin kai.
A ranar 18 ga wannan watan da muke ciki ne yakamata Machar ya dawo birnin Juba, amma a sai ranar 19 wato jiya kenan majiyarsa mataimakin shugaban kasar ta bayyana cewa an dage dawowarsa birnin Juba har illah ma sha'alla. Majiyar ta kara da cewa gwamnatin shugaban Silver Kiir ce take jinkirta dawowarsa birnin.
Amma majiyar gwamnatin Juba kuma ta bayyana cewa Riek Machar yana son shigo da makamai masu yawa a cikin birnin tare da shi , fiye da yadda yerjejniyar da suka cimma ta kayyade masa.
Dubban mutanen kasar ne aka kashe tun watan decemban shekara ta 2013 kuma wasu miliyoyi suka kauracewa gidajensu a cikin kasar.