Sudan Ta Koka Kan Matsalar Fataucin Kananan Yara A Yankin Gabashin Afrika
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4195-sudan_ta_koka_kan_matsalar_fataucin_kananan_yara_a_yankin_gabashin_afrika
Ministan harkokin cikin gidan kasar Sudan ya koka kan yadda matsalar fataucin mutane musamman kananan yara ke ci gaba da habaka a yankin gabashin Afrika.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 21, 2016 12:49 UTC
  • Sudan Ta Koka Kan Matsalar Fataucin Kananan Yara A Yankin Gabashin Afrika

Ministan harkokin cikin gidan kasar Sudan ya koka kan yadda matsalar fataucin mutane musamman kananan yara ke ci gaba da habaka a yankin gabashin Afrika.

Shafin Al-Yaumus-Sabi'i ya watsa rahoton cewa; Ministan harkokin cikin gidan kasar Sudan Ismat Abdur-Rahman Zainul-Abideen ya koka kan matsalar habakar fataucin mutane musamman kananan yara tare da kokarin mai da kasarsa tamkar hanyar shiga da su cikin kasashen gabashin Afrika.

Zainul-Abideen ya kara da cewa; Gwamnatin Sudan tana da karfin da zata iya shawo kan matsalar fataucin mutanen tare da kawo karshensa domin a halin yanzu haka ma ta jibge jami'an tsaronta a kan dukkanin hanyoyin da ake amfani da su wajen safarar mutanen.

Har ila yau ministan harkokin cikin gidan kasar ta Sudan ya yi gargadi kan masifar da ta kunno kai a tsakanin daliban jami'ar kasar ta yin amfani da muggan kwayoyi musamman a tsakanin matasa.