Kungiyar Boko Haram Ta kai Hari A Wani Kauyen Borno
Kimanin Mutane 4 ne suka rasu sanadiyar Harin Ta'addanci da Kungiyar Boko Haram ta kai kauyen Mairi dake jihar Borno na arewa masu gabashin Najeria
Kafar watsa labaran Alyaumu Sabi'i ta Kasar Masar ta nakalto wani daga cikin shugabanin kauyen na cewa maharan sun yi amfani da babura wajen kai harin, inda da shigar su cikin kauyen suka buda wuta kan Al'umma tare kuma sanya wuta a gidajen mutane, harin da ya yi sanadiyar mutuwar Mata uku tare da wani magidanci guda.
Wannan hari na zuwa ne maku guda kacal, bayan wani mumunan hari da kungiyar ta Boko haram ta kai kauyen Dalori na kusa da garin Maiduguri, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 85.
A nasa bangare, Baba Kaka Garba daya daga cikin dattijan kauyen ya tabbatar da mutuwar mutanan 4, inda ya ce Mata ukun da suka rasu, suna cikin gidajensu a yayin da mayakan boko haram suka sanyawa gidajen nasu wuta, shi kuma mutuman guda ya rasu bayan da maharan suka bude masa wuta.