An kashe Mayakan Ashabab uku a kudu masu yammacin Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4234-an_kashe_mayakan_ashabab_uku_a_kudu_masu_yammacin_somaliya
Wani Jami'in Sojin Samaliya ya sanar hallaka mayakan Ashabab akalla guda uku a yayin wani farmaki da dakarun tdaron kasar gami da na kungiyar Tarayyar Afirka suka kai yankin Bakul dake kudu maso yammacin Kasar
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 22, 2016 10:48 UTC
  • An kashe Mayakan Ashabab uku a kudu masu yammacin Somaliya

Wani Jami'in Sojin Samaliya ya sanar hallaka mayakan Ashabab akalla guda uku a yayin wani farmaki da dakarun tdaron kasar gami da na kungiyar Tarayyar Afirka suka kai yankin Bakul dake kudu maso yammacin Kasar

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa na kasar China daga birnin Magadushu ya nakalto Abdi Muhamad Diyale daya daga cikin shugabanin Sojojin kasar Somaliya a yau juma'a na cewa a wani farmaki da dakarun hadin gwiwa na kasar da na kungiyar Tarayyar Afirka suka kai sun samu nasarar kwato kauyukan Gobato, War-cadey da Gumuro mai nisan kilomita 45 dake arewa maso gabashin garin Wajid daga hanun kungiyar Ashaban mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida, har ila yau rahoton ya ce bayan hallaka mayakan kungiyar guda uku an jikkata wasu hudu na daban.

Babban jami'in sojin Somaliyan ya tabbatar da cewa za a ci gaba da kai farmaki domin 'yanto sauran yankunan da har yanzu ke kalkashin ikon kungiyar Ashabab.