Nadin Sabon Firaministan Kasar D/Congo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4267-nadin_sabon_firaministan_kasar_d_congo
Shugaban Kasar D/Congo ya nada sabon Firaminista
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 23, 2016 23:30 UTC
  • Nadin Sabon Firaministan Kasar D/Congo

Shugaban Kasar D/Congo ya nada sabon Firaminista

Jaridar Le Figaro ta kasar Faransa ta habarta cewa Ajiya Assabar Shugaban Kasar D/Congo Denis Sassou Nguesso ya nada Clemant Mouamba a matsayin sabon Firaministan kasar, hakan kuwa na zuna ne maku guda da rantsuwa kama aiki na Shugba Nguesso da ta gudana a ranar 16 ga watan Avrilun da ya gabata.

Duk da irin korafe korafen da aka gabatar, a karshe Kotun kundin tsarin milkin kasar ta sanar da Shugaba Denis Sassou Nguesso a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar da ya gudana a ranar 20 ga watan Maris din ya gabata, inda ya samu kashi 60,19% na kuri'un da aka kada a kasar.