Mayakan Al'Qaeda sun sako yar kasar Austria da suka sace a Burkina
Hukumomin Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar sun sanar a yau lahadi cewa Jocelyn Elliot yar kasar Austria da yan Alqaeda suka sace ta samu gubuta daga hannun su.
Mayakan na Alqaeda sun dai sace wannan mata tareda mijinta wani jami’in kiwon lafiya a farkon watan janairu shekarar bana a wani gari mai suna Djibo dake kasar Burkina Faso.
An dai sako matar ne ba tareda an biya kudin fansa ba inji Ministan harakokin wajen kasar Burkina Faso Alpha Barry, inda ya ci gaba da cewa matar da aka sallamo ta samu ganawa da shugaban Nijar Mahamadu Issifou kuma tana cikin koshin lafiya.
Kasar Australiya ta yaba da kokarin da kasashen Burkina Faso da Nijar wajen gani an sako wannan mata duk da yake ana sa ran yan kungiyar Al’Qaeda za su sako mijin matar mai suna Arthur Kennet Elliot dan shekaru 82 a nan gaba.