Fashewar Bom A arewa maso gabashin Najeria
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4276-fashewar_bom_a_arewa_maso_gabashin_najeria
Fashewar Bam ya yi sanadiyar asarar rayuka a arewa maso gabashin Najeria.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 24, 2016 00:54 UTC
  • Fashewar Bom A arewa maso gabashin Najeria

Fashewar Bam ya yi sanadiyar asarar rayuka a arewa maso gabashin Najeria.

Kafar watsa labaran Afirka Time ta nakalto Sani Usman Kukasheka mai magana da yawun Rundunar Sojin Kasar Najeria na cewa a ranar Larabar da ta gabata wani Bom ya tashi a kusa da sansanin 'yan gudun hijra na garin Banki dake kusa da kan iyakar Najeria da Kamaru, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 7 tare da jikkata wasu 9 na daban.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin kai harin, saidai ana zarkin kungiyar boko Haram, ganin cewa sama da shekara guda zuwa yanzu kungiyar ta fadada kai hare-harenta a yankunan dake kai iyakokin kasashen Najeria, Niger , Kamaru da kuma Tchadi.

Baya ga haka kungiyar ta Boko Haram na kai hare-haren ta'addancin a Masallatai, kasuwancin da suke da yawan tsukoson Mutane,tashoshin manyan Motoci da kanana gami da guraren bincike na jami'an tsaro.