Sudan: Yankin Darfur Zai Ci Gaba Da Zama Yadda Yake
Rahotanni daga kasar Sudan sun bayyana cewar sakamakon zaben raba gardamar da aka gudanar a kan matsayin yankin Darfur na kasar Sudan na nuni da cewa mafi yawa daga cikin al'ummar yankin sun goyon bayan yankin ya ci gaba da zama a matsayin da yake a yanzu.
Hukumar zaben kasar ta Sudan ta ce kashi 97.72 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben raba gardamar sun amince da yankin ya ci gaba da wanzuwar jihohi biyar da ake da su a yanzu, maimakon hade shi a matsayin jiya guda kamar yadda 'yan tawaye da sauran kungiyoyi na 'yan adawa suke so wanda suka ce hakan ne zai kara ba wa yankin 'yancin cin gashin kai da suke so.
Gwamnatin Sudan din dai ta gudanar da zaben raba gardamar ne inda ta ce ta ba wa al'ummar yankin zabi ne tsakanin ci gaba da wanzuwar yankin na Darfur yadda yake a halin yanzu ko kuma hade su a matsayin jiha guda daya; zaben da 'yan tawaye da 'yan'adawa suka kaurace masa
Gwamnatin ta Sudan dai tana fatan kuri'ar raba gardamar zai kawo karshen tashin hankalin da aka shafe kimanin shekaru 13 ana yi da yayi sanadiyyar mutuwar mutane kusan dubu 300 da kuma wasu sama da miliyan biyu da rabi da suka rasa matsugunansu.