RDC : 'Yan Adawa Na Kara Matsin Lamba Ga Gwamnati
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4327-rdc_'yan_adawa_na_kara_matsin_lamba_ga_gwamnati
'Yan hammayya a jamhuriya demukuradiyyar Congo na ci gaba da kara matsin lamba ga masu mulki akan mutunta kudin tsarin mulkin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:10+00:00 )
Apr 25, 2016 00:32 UTC
  • Shugaban Jamhuriya demukuradiyyar Congo, Joseph Kabila.
    Shugaban Jamhuriya demukuradiyyar Congo, Joseph Kabila.

'Yan hammayya a jamhuriya demukuradiyyar Congo na ci gaba da kara matsin lamba ga masu mulki akan mutunta kudin tsarin mulkin kasar.

Yan adawa a wannan kasar sun gudamnar da wani ganganmi a Kinshasa domin nuna adawa ga anniyar shugaba Joseph Kabila na neman yin kwaskwarima ga kundin zabe domin ci gaba da mulki..

Mayan jam'iyyun adawa na kasar da suka hada da MLC da UNC dama wasu kananan jam'iyyu na son a gudanar da zaben kamar yadda doka ta tanada a karshen wannan Shekara.

A karshen watan Nowamban bara ne Mr Kabila ya bayana anniyar sa ta kiran wani taron muhawara na kasa domin cimma matsaya kan jadawalin mayan zabubukan kasar, saidai har kawo yanzu babu wata matsaya da aka cimma.