Sudan Ta Kudu : An Damu Kan Rashin Komawar Mashar A Juba
-
jogoran yan tawaye Sudan ta Kudu Riek Masha.
Duniya na ci gaba da nuna damuwa akan rashin komawar jagoran 'yan tawayen Sudan ta Kudu Riek Machar birnin Juba, matakin da zai kai ga aiwatar da yerjejeniyar samar da zamen lafiya a wannan kasa.
A wannan Asabar ce Mr Machar ya kamata ya isa birnin Juba, ta jirgin sama daga kasar Habasha, domin shiga gwamnatin wucin gadi ta kasar, a matsayin mataimakin shugaba Salva Keer saidai a cewar sa bai samu izinin sauka ba daga gwamnatin Sudan ta Kudu.
Tuni dai aka fara saka ayyar tambaye cewa ko bangarorin biyu na shirye domin aiwatarda yerjejeniyar sulhu da aka cimma a shiga tsakanin MDD.
Yayin da kwamitin tsaro na MDD ke shirin gudanar da wani zama a gobe da nufin kakabawa bangarorin biyu takunkumi kan kawo cikas ga wunkurin kawo karshen yaki a wannan kasa, ita kuwa Amurka na zargin gwamnatin Salva Keer da hana Mr Masha shiga Juba.
A wani labari a yau ne ake sa ran Mr Mashar zai isa Juba, bayan rashin samun isa kasar a karo na uku.