Yan Adawa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Jamhuriyar DR COngo
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4375-yan_adawa_sun_gudanar_da_zanga_zangar_lumana_a_jamhuriyar_dr_congo
Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun gudanar da zanga-zangar lumana domin jaddada rashin amincewarsu da duk wani shirin tazarcen shugaba Joseph Kabila a kan karagar shugabancin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:58:11+00:00 )
Apr 25, 2016 13:41 UTC
  • Yan Adawa Sun Gudanar Da Zanga-Zangar Lumana A Jamhuriyar DR COngo

Yan adawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun gudanar da zanga-zangar lumana domin jaddada rashin amincewarsu da duk wani shirin tazarcen shugaba Joseph Kabila a kan karagar shugabancin kasar.

Yan adawar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun fito zanga-zangar ce a yau Litinin a babban birnin kasar Kinshasa domin jaddada rashin amincewar da duk wani shirin mahukuntan kasar na kokarin ganin Joseph Kabila ya yi tazarce a kan karagar shugabancin kasar tare da jaddada adawarsu kan duk wani shirin dage lokacin zaben shugaban kasa saboda wasu dalilai marassa tushe.

Har ila yau 'yan adawar Jamhuriyar Dimokaradiyyar ta Congo sun bayyana rashin amincewarsu da duk wani zaman tattaunawa da gwamnatin kasar kan batun neman dage zaben shugaban kasa. Shugaba Joseph Kabila dai ya bukaci dage zaben shugaban kasa tare da shiga zaman tattaunawa da jam'iyyun adawar kasar da nufin samar da kyakkyawar hanyar zabe a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo amma har yanzu wannan buri nashi bai samu karbuwa ba daga bangaren 'yan adawar kasar.