Harin 'yan bindiga a wani kauyen Najeria
Wasu 'yan bindiga sun kashe Mutane 7 a wani kauye dake kudu maso gabashin Najeria
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Legas ya nakalto wani jami'in 'yan sandar Jihar Enugu dake kudu maso gabashin kasar, a wannan talata na cewa 'yan bindigar sun shiga kauyen ne cikin kayan farar hula yayin da suka boye makaman da suke tare da su, inda suka buda wuta kan mutanan kauyen tare da kashe 7 daga cikin su sannan kuma suka jikkata wani adadi mai yawa.
A ranar Lahadin da ta gabata ma wasu 'yan bindigar sun kai hari a kauyen Nimbou inda suka kashe wani adadi daga cikin manoman garin tare da kwashe dukiyiyinsu.
An kai harin ne a cikin dare yayin da mutanan kauyen ke kwana.
Irin wannan hari dai ba wani sabon abu ba ne a Najerian, inda barayi shanu suka saba kai hari kan makiya tare da kwashe dukiyoyinsu.
A shekarar da ta gabata irin wannan hari ya lashe rayukan mutane sama dari a kauyukan dake kudu masu gabashin kasar.
Harin barayi, ko na kabilanci na lashe rayukan mutane da dama a Najeria.