Gwamnatin Kasar Ivory Coast Ta Jaddada Aniyarta Ta Fada Da Ta'addanci
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i445-gwamnatin_kasar_ivory_coast_ta_jaddada_aniyarta_ta_fada_da_ta'addanci
Gwamnatin Ivory Coast ta yi kira ga sauran kasashen yankin yammacin Afrika kan daukan matakan karfafa yaki da ayyukan ta'addanci a yankin.
(last modified 2018-08-22T06:57:47+00:00 )
Feb 07, 2016 14:28 UTC
  • Gwamnatin Kasar Ivory Coast Ta Jaddada Aniyarta Ta Fada Da Ta'addanci

Gwamnatin Ivory Coast ta yi kira ga sauran kasashen yankin yammacin Afrika kan daukan matakan karfafa yaki da ayyukan ta'addanci a yankin.

Ministan mai kula da harkokin alaka tsakanin kasashen Afrika a gwamnatin Ivory Coast Ali Coulibaly ya jaddada yin kira ga kasashen yankin yammacin Afrika da su kara matsa kaimi a fagen yaki da ta'addanci da nufin kawo karshen wannan masifa a yankin baki daya.

Coulibaly ya kara da cewa: Baya ga masifar ayyukan ta'addanci a nahiyar Afrika, akwai kuma matsalar 'yan gudun hijira musamman matasa da suke halaka a teku a kokarin da suke yi na shiga cikin kasashen nahiyar Turai lamarin da ya zame dole a nemo hanyar magance wannan matsala cikin hanzari.