Alkalluman fararren hula dake mutuwa ya karu a Najeriya
Kungiyar AOAV mai yin nazari na tashin hanakali ta ce alkallumar fararen hular da suka mutu sanadiyar harin kungiyar Boko Haram a Najeria ya karu a shekarar da ta gabata.
Rahoton da kungiyar ta fitar a Najeriya na cewa an samu karuwar alkaluman fararren hula dake rasa rayukansu a shekarar 2015 a kasar, fiye da shekarun hudu da suka gabata.
Kungiyar mai suna AOAV, ta ce hakan ya biyo bayan hare-haren kunar bakin wake da mayakan Boko Haram ke kaiwa musamman a yankin arewa maso yammaci kasa.
AOAV ta ce yawan mamata da kuma wadanda ke samun rauninka ya karu da kashi 190 fiye da yadda al’amarin yake a shekarun baya, Kuma Kashi 76 cikin 100 na mamatan farraren hula ne.
Rahoton ya ce yadda kungiyar ta boko haram ke amfani da dasa bama-bamai a kasuwanni, tashar motoci , masallatai da kuma guraren taruwa Jama'a, da kuma yadda suke amfani da manyan makamai wajen kai hari shi ne ya yi sanadiyar karuwar alkalluman.