Nijar : Nuna Adawa Da Takurawa Kungiyoyin Fararen Hula
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i4483-nijar_nuna_adawa_da_takurawa_kungiyoyin_fararen_hula
Nuna Adawa Da Takurawa Kungiyoyin Fararen Hula
(last modified 2018-08-22T06:58:11+00:00 )
Apr 28, 2016 07:55 UTC
  • Nijar : Nuna Adawa Da Takurawa Kungiyoyin Fararen Hula

Nuna Adawa Da Takurawa Kungiyoyin Fararen Hula

Kungiyoyin Fararen Hula A Jamhuriyar Nijar Sun yi tir da yadda hukuma ta ke takurawa kungiyoyin su da hana su aiwatar da ayyukansu.

Radiyon Kasa da kasa na Faransa ya ce a yau alhamis ne kungiyoyin farar hular na jamhuriyar Nijar su ka fitar da wani bayani da a ciki su ka bayyana cewa; An take mu su hakkokinsu mafi karanci da su ka hada da yin zanga-zanga.

Bugu da kari bayanin ya kunshi yin kira ga al'ummar kasa ta Nijar da fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin zanga-zanga a gobe bayan idar da sallar juma'a domin yin Allah wadai da yi wa demokradiyya karen tsaye.

A ranar lahadin da ta gabata ne dai mahukuntan kasar su ka hana gudanar da Zanga-zangar da wata kungiyar farar hula ta shirya.